BiuBlog


PROMOTE MUSIC | ADVERTISE | SUBMIT FREEBEAT

Popular Posts

Powered by Blogger.

Search This Blog

raintemplates-t6

raintemplates-t4

raintemplates-t2

Header Ads

Social Media

raintemplates-t4

raintemplates-t7

raintemplates-t3

raintemplates-t7

raintemplates-t1

Social Media

Facebook Fanpage

raintemplates-t5

raintemplates-t3

raintemplates-t5

Popular Posts

  • Kare musulman China ya jawo ma Ozil haramcin wasan PES daga Kasar China.

    NOTE:- If you are having problem in Downloading our file Try and use Opera mini
    Kare musulman China ya jawo ma Ozil haramcin wasan PES daga Kasar China.

  • An cire dan wasan tsakiya na Arsenal Mesut Ozil daga cikin wasan bidiyo na kwamfuta na Pro Evolution Soccer 2020 samfurin na China sakamakon sukar da ya yi wa hukumomin kasar na gallaza wa Musulmi 'yan kabilar Uighur. Ozil, wanda Musulmi ne ya kira 'yan kabilar ta Uighur "mayakan da suka bijire wa gallazawa''. Dan wasan ya kuma soki China da shirun da Musulmi suka yi kan abin da kasar take yi wa mutanen. Kamfanin NetEase, wanda ke yin samfurin wasan a China ya ce an cire tsohon dan wasan na Jamus daga wasannin uku da ake da su yanzu a kasar. A wata sanarwa da kamfanin ya fitar wadda ke nuna dalilinsa na daukar matakin ya ce: "Dan wasan na Jamus ya sanya maganganu masu tsauri a kan China a shafin intanet," Sanarwar ta kara da cewa: "Kalaman sun bata wa magoya baya 'yan China rai kuma sun saba al'adar kauna da zaman lafiya ta wasanni. Ba za mu lamunta da haka ba." A dangane da kalaman na Ozil, kungiyar dan wasan, Arsenal ta ce it aba ta da alaka da wata siyasa, sannan kuma ma'aikatar harkokin wajen China ta ce an yaudari dan wasan mai shekara 31, wanda dan asalin Turkiyya ne da labaran karya. Kungiyoyin kare hakkin dana dam sun ce kusan mutane miliyan daya ne, yawancinsu Musulmi 'yan kabilar ta Uighur, suke ganin ana tsare da su a sansanoni masu tsananin tsaro a China ba tare da an yi musu shari'a ba. Ita dai China a kullum tana musanta zargin da ake yi mata na gallaza wa Musulmin 'yan kabilar Uighur a kasar, inda take cewa tana ilmantar da su ne a wasu sansanoni na koyar da sana'o'in hannu domin raba su da akidar tsananin kishin addini. Babban Sakataren kungiyar al'ummar Musulmi ta Birtaniya, Harun Khan, ya ce kalamin na Ozil abin yabawa ne matuka, kuma ya bayyana matakin Arsenal na nesanta kanta daga ra'ayin dan wasan a matsayin abin kaico.

    No comments:

    Post a Comment

POPULAR POSTs


Pages


ADVERTISE | CONTACT US